”
#2754HadeethEnc[Ingantacce ne]
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Manzon Allah SAW ya Kasance yana E'itikafi a cikin goman kowane Azumin Ramadan, to yayin da shekarar da aka karbi ransa ta zo yayi E'itikafi kwana Ashirin"
”
#3015HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullah bin Omar - Allah ya yarda da shi - a cikin marfoo: "Bilal yana kiran dare, don haka ku ci ku sha har sai kun ji kiran da Ibn Umm Maktoum ya yi."
”
#3449HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Mu'azah ta ce : Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce: Shin ke baharuriyyace? na ce: Ni ba baharuriyya ba ce, sai dai tambaya nake. Ta ce: Hakan yana samunmu, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu…
”
#3546HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku…
”
#3738HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a…
”
#3755HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa.
”
#4196HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
”
#4202HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"
”
#4436HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".
”
#4438HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".
”
#4439HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce " Mun kasance tare da Annabi - Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin wata tafiya a cikinmu wasu suna Azumi , wasu kuma basa yi, ya ce gida gida a cikin rana mai zafi, kuma muka yawaita shiga Inuwa Ma'ab…
”
#4457HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.