Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".
Explanation
Benefits
Allah Ya ware wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna guda takwas ga masu azimi, idan suka shiga ta kofar sai akulleta.
Bayanin cewa aljanna tana da ƙofofi.
Sindi ya ce: Faɗinsa: (Ina masu azimi), wato masu yawaita yin azimi kamar mai adalci da azzalimi, ana faɗin haka ga wanda ya saba da hakan, ba ga wanda ya aikata sau ɗaya ba kawai.
(al-Rayyan) yana nufin wacce take ƙosarwa; domin cewa masu azimi suna jin ƙishirwa musammanma dai acikin kwanukan bazara masu tsawo masu zafi; sai a yi musu sakayya da ambatan wannan ƙofar da abinda yake keɓantarsu da shi da sunan ƙofar Arrayyan, kuma an ce Arrayyan wato Fa'alan mai yawan ƙoshi kishiyar ƙishirwa, an anbaceta da shi; domin cewa ita sakamakon masu azimi ce saboda ƙishirwarsu da kuma yunwarsu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

