Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah?
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Mu'azah ta ce : Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce: Shin ke baharuriyyace? na ce: Ni ba baharuriyya ba ce, sai dai tambaya nake. Ta ce: Hakan yana samunmu, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
Explanation
Benefits
Haruriyya an dangantasu ga wani gari kusa da Kufa, sunansa "Hiraura’a'; wasu jama'a ne daga Khwarijawa, ta kamantata da su ne saboda tsanantawarsu a cikin al'amarinsu da kuma yawan tayambayarsu da ta'annitancinsu da ita.
Malami ya bayyanawa wanda ya neme shi dan neman sani da kuma neman shiriya.
Bada amsa da nassi ya fi; domin cewa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - bata bijiro da ma'anar da mai tambayar ta tambayeta ba; hakan domin cewa amsa da nassi ya fi yanke musu.
Sallamawa hukuncin Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda bawa bai san hikimar ba.
Nawawi ya ce: Ma'anar faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa wasu jama'a daga Khwarij suna wajabtawa mai al’ada rama sallar da ta wuce a lokacin al’ada, wannan kuwa saɓanin Ijma'in musulmai ne, wannan tambayar da Nana A'isha ta tambayeta tambaya ce ta inkari wato: Wannan hanyar Haruriyya ce tir da wannan hanyar.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

