Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah
Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce : Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai k…

