Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Cewa Ummu Habiba 'yar Jahsh wacce take ƙarƙashin Abdurrahman Dan Awf ta kawo koken (zubar) jini ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce mata: "Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka". Ta kasance tana wanka a kowacce sallah.
Explanation
Benefits
Mai jinin cuta tana daukar kanta mai haila gwargwadan kwanukan da haila taka zo mata a cikinsu, kafin abinda ya sameta ya sameta na jinin cuta.
Idan gwargwadan kwanukan al'adarta na asali suka shude, to ita ana daukarta mai tsarki daga al’ada - koda cewa jinin cuta yana tare da ita - sai ta yi wankan daukewar jinin al’ada.
Mai jinin cuta wanka ba ya wajaba akanta a kowacce sallah; domin wankanta - Allah Ya yarda da ita - ya kasance da ijtihadi ne daga gareta, da a ce ya kasance wajibi ne da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mata shi.
Alwala tana wajaba akan Mai jinin cuta a kowacce sallah; domin hadasinta madawwami ne ba mai yankewa ba ne, misalinta dukkan wanda karinsa madawwami ne kamar wanda a tare da shi akwai yoyon fitsari, ko fitar tusa mai a koyaushe.
Tambayar ma'abota ilimi daga abinda yake rikitarwa a al'amuran Addini, yayin da wannan matar ta kawo kuka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta tambaye shi game da yawan jinin da yake samunta.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

