Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".
Explanation
Benefits
Wanzuwar alheri a cikin mutane saboda biyayyarsu ne ga Sunnah, kuma ɓacin al'amura yana ratayane da canja sunna.
Saɓawa mazawa littafi (Yahudawa da Nasara) da 'yan bidi'a, domin cewa su suna jinkirta buɗa baki.
Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai bayanin sababin hakan, Muhallab ya ce: Hikima a cikin hakan kada a yi ƙari a yini a dare, kuma ya fi tausayi ga mai azimi kuma ya fi ƙarfafa gare shi akan ibada, malamai sun haɗu akan cewa mahallin hakan idan faɗuwar rana ta tabbata da gani (faɗuwar rana) ko da labartawar adalai biyu, haka adali ɗaya a zance mafi rinjaye.
Ibnu Hajar ya ce: Faɗakarwa: Daga bidi'o'i ababen ƙi abinda aka farar a wannan zamanin na yin kiran sallah na biyu kafin Asuba da kwatankwacin ɗaya bisa uku na awa a cikin (watan ) Ramadan, da kashe fitilun da aka sanya su alama dan haramta ci da sha ga wanda yake nufin yin azimi dan riyawa daga wanda ya farar da shi cewa shi dan tsare ibada, kuma babu wanda ya san hakan sai ɗaiɗaikun mutane, haƙiƙa hakan ya jasu zuwa sun kasance ba sa kiran sallah sai bayan faɗuwar rana da daraja dan tabbatar da lokaci a yadda suka riya, sai suka jinkirta buɗa baki, kuma suka gaggauta sahur, suka saɓawa Sunnah, saboda haka alheri ya karanta a garesu kuma sharri ya yawaita a cikinsu, Allah ne abin neman taimako.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

