Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".
Explanation
Benefits
Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan azimin nafila.
Wajabcin ikhlasi da neman yardar Allah, kuma kada ya yi azimi dan riya ko jiyarwa ko dan wasu manufofin daban.
Sindi ya ce: Faɗinsa (A tafarkin Allah), za'a iya ɗaukar cewa abin nufi mujarradin gyara niyya, kuma za'a iya ɗaukar cewa abin nufi da shi cewa shi ya yi azimi a halin kasancewarsa mai yaƙi, na biyun shi ne abin gaggawar (manufa).
Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Kharif saba'in) Kharif wani lokaci ne sananne a shekara, abin nufi da shi a nan shekarar (gaba ɗayanta), kuma keɓance Kharif (Kaka) da ambato banda ragowar lokutan - zafi da sanyi da damina -; domin cewa Kharif (Kaka) ya fi ragowar lokutan kyau domin kasancewarsa ana tsinkar 'ya'yan itatuwa a cikinsa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

