Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci.
Explanation
Na farko: Azimin kwana uku a kowane wata.
Na biyu: Raka'a biyu ta walaha a kowace rana.
Na uku: Witiri kafin bacci; hakan ga wanda ya ji tsoron kada ya farka a ƙarshen dare.
Benefits
Ibnu Hajar al-Askalani ya faɗa acikin faɗinsa: Azimin kwana uku daga kowane wata, abinda yake bayyana cewa abin nufi da su kwanukan fari; sune: Ranar goma sha uku, da goma sha huɗu, da goma sha biyar, daga watan Hijira.
Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: A cikinsa akwai son gabatar da witiri kafin bacci, hakan a cikin hakkin wanda bai aminta da farkawa ba.
Muhimmancin waɗannan ayyukan guda uku; saboda wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wani adadi daga sahabbansa.
Ibnu Daƙiƙul id ya faɗa a cikin faɗinsa: (Da raka'o'i biyu na walaha): Wataƙila cewa shi ya ambaci mafi ƙaranci ne wanda ake samun ƙarfafawa a aikata shi, a cikin wannan akwai nuni akan son sallar walaha, kuma cewa mafi ƙarancinta raka'a biyu ce.
Lokacin sallar walaha: Tun daga ɓullowar rana da kimanin ɗaya bisa huɗu na awa (kwata), kuma lokacinta yana miƙewa har zuwa kusan kafin lokacin azahar da minti goma, adadinta: Mafi ƙarancinta raka'a biyu ce, an yi saɓani a mafi yawanta; An ce: Raka'a takwas ce, ance: Babu iyaka ga mafi yawanta.
Lokacin witiri: Tun daga bayan sallar isshai'i har zuwa ɓullowar alfijir, kuma mafi ƙarancinsa raka'a ɗaya ne, mafi yawancinsa raka'a goma sha ɗaya ne.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

