KOYON RUBUTUN LARABCI JUZU IN AMMA MUSHAFIN ALQUR ANI
LITTAFIN KOYON RUBUTUN LARABCI, DA KUMA JUZ'U AMMA (IZU BIYU) DAGA ALKUR'ANI (تعلم الخط العربي وجزء عم من المصحف): Littafi ne da harshen LARABCI wanda Dr. Haisam Sarhaan ya wallafa shi, da manufar koyar da nau'in rubutun KHADDUN NASKH, ta hanyar bi sannu-sannu wajen koyan rubuta harrufan larabci a dukkan halin da suka zo a cikinsu mabanbanta (farkon kalma, tsakiyar kalma, da karshenta), Daga nan, sai kokarin gwaji ko dabbaka hakan akan zababbun littatafan ilimi, kamar...
KOYON RUBUTUN LARABCI JUZU IN AMMA MUSHAFIN ALQUR ANI
LITTAFIN KOYON RUBUTUN LARABCI, DA KUMA JUZ'U AMMA (IZU BIYU) DAGA ALKUR'ANI (تعلم الخط العربي وجزء عم من المصحف): Littafi ne da harshen LARABCI wanda Dr. Haisam Sarhaan ya wallafa shi, da manufar koyar da nau'in rubutun KHADDUN NASKH, ta hanyar bi sannu-sannu wajen koyan rubuta harrufan larabci a dukkan halin da suka zo a cikinsu mabanbanta (farkon kalma, tsakiyar kalma, da karshenta), Daga nan, sai kokarin gwaji ko dabbaka hakan akan zababbun littatafan ilimi, kamar yadda littafin yake da manufar koyar da nau'in rubutun da aka masa lakabi da KHADDUL USMANIY, wanda shine nau'in rubutun da aka rubuta Mus-haf (Alkur'ani) a zamanin khilafancin Usman -Allah ya kara yarda a gare shi- za a koyar da nau'in rubutun ne ta hanyar kokarin dabbaka hakan ga juz'u Amma (جزء عم). Littafi ne mai dadi mai ban kaye, wanda yake dacewa da kowane Mutum kamar kananan yara da manya, da masu magana da harshen Larabci, da wadanda suke magana da sauran yarukan; suke son koyan Larabcin.
ALKUR'ANI shine fiyayyen zance, saboda kasancewarSa Maganar Allah, wanda Ya saukar da Shi ta hanyar mafificin Mala'ika; wato (Jibrilu Alaihis Salaamu), a zuciyar fiyayyen Manzanni; wato annabi (Muhammadu Sallal Lahu Alaihi Wa Sallama), a mafificin gari, wato (Makkatul Mukarramah), a mafificin zamani, wato watan (Ramadhana), a cikin mafificin dare, wato (daren Lailatul Kadari), da mafificin yare, wato (harshen Larabci).
Allah ya kure jinsin Mutum da Aljan akan su zo da kwatankwacin sura daya misalin Alkur'ani, sai suka gaza yin hakan; basu iya ba. Kuma Allah ya dauki nauyin kiyaye Alkur'ani, don haka; babu wanda zai iya kara harafi daya a cikinSa ko ya rage, a fadi da tsawon zamani. Kuma Alkur'ani surori dari da goma sha hudu ne (114); daga suratul Fatiha zuwa suratun Naasi. Kuma Allah ya sanya karatun Alkur'ani ya zamto bautar da ake neman karin kusanci gare Shi Ta'alah; a inda Ya sanya karatun harafi daya yake da lada goma.
koyon rubutun larabci
KOYON RUBUTUN LARABCI JUZU IN AMMA MUSHAFIN ALQUR ANI
Scan QR Code | Use a QR Code Scanner to fast download directly to your mobile device