Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi
Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance muna kiwon raƙuma sai zagayena ya zo sai na korosu garke da daddare sai na riski Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsaye yana karantar da mutane sai na riska faɗinsa: "Babu wan…

