((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.
((An karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi yace Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aik…

