Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
Explanation
Benefits
Muhimmanicin kiyaye sallah, ita ce haske ga bawa a duniya da kuma ranar alkiyama.
Sadaka dalili ce akan gaskiyar imani.
Muhimmancin aiki da Alkur’ani da gasgata shi, dan ya zama hujja a gareka ba akanka ba.
Rai idan ba ka shagaltar da ita da da'a ba, za ta shagaltar da kai da sabo.
Kowanne mutum ba makawa sai ya yi aiki; kodai ya 'yanto ransa da biyayya (ga Allah) ko ya halakar da ita da sabo.
Hakuri yana bukatar juriya da neman lada, kuma acikinsa akwai wahala.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

