(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».
Explanation
Benefits
Ibnu Hajar ya ce a cikin faɗinsa: "A cikin inuwarSa": An ce abinda ake nufi: Inuwar Al’arshinsa, Hadisin Salman yana nuni a kansa daga (riwayar) Sa'id ɗan Mansur da Isnadi kykkyawa: "Mutum bakwai Allah Zai inuwantar da su a cikin inuwar al-ArshinSa".
Ibnu Hajar ya ce: Mafi kyan abinda aka fassara mai adalci da shi cewa shi ne wanda yake bin umarnin Allah ta hanyar ajiye kowane abu a bigiransa ba tare da wuce gona da iri ko sakaci ba, kuma ya gabatar da shi a ambato dan gamewar amfanin da shi.
Falalar jiran sallah bayan sallah.
Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan soyayya saboda Allah da bayanin girman falalarta.
An keɓanci matsayi da kyau dan tsananin kwaɗayin mutane a cikinsu da kuma kwaɗayinsu a kansu, da wahalar samunsu.
Abinda ya fi a sadaka shi ne ɓoyewa da nisanta daga riya, duk da an halatta bayyanar da sadaka da zakka idan sun kuɓuta daga riya kuma aka nufi kwaɗaitar da wani akan ciyarwa kuma dan waninsa ya yi koyi da shi, da kuma bayyanar da alamomin Musulunci.
Kaɗai waɗannan mutum bakwan sun samu wannan ni'imar ce saboda ikhlasi ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma saɓawa son rai.
Faɗinsa: "Mutum bakwai Allah Zai inuwantar da su": Taƙaitawarsu da wannan adadin ba abin nufi bane, kai wasun waɗannan nau'ikan sun zo a cikin hadisin daga waɗanda Allah Zai inuwantar da su a inuwar Al’ArshinSa.
Ibnu Hajar ya ce: Ambatan maza a cikin hadisin ba shi da wani abin fahimtar cewa su ake nufi kawai; kai mata ma suna tarayya tare da mazan a cikin ayyuka a abinda aka ambata, sai dai idan ana nufin shugaba adali wato babban shugabanci, inba haka ba to mace zata iya shiga tunda itama tana da iyalai kuma ta yi adalci a cikinsu, kuma ɗabi'ar lazimtar masallaci ta fitar da mace; domin cewa sallar mace a cikin gidanta ya fi ta yi a masallaci, abinda ke koma bayan hakan to tarayya da su ta tabbata, har namijin da mace ta neme shi shima ana suranta samun hakan a macen da sarki kyakkyawa ya nemeta a misali sai taƙi dan jin tsoron Allah - Madaukakin sarki - tare da cewa tana bukatar hakan.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

