Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Safina - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala.
Explanation
Benefits
An so ƙaranta ruwan alwala da wanka gwargwadan buƙata, kuma wannan ita ce shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Abin nufi cikawa a alwala da wanka tare da kula da sunnoni da ladubba ba tare da ɓarna ko ƙwauro ba, kuma a kiyaye lokaci da yawan ruwan da ƙarancinsa da wanin hakan.
Ana anbaton janaba ga dukkan wanda ya fitar da maniyyi ko ya yi jima'i, kuma an anbaceta da hakan dan mai ita yana nisantar sallah da ibadu har sai ya tsarkaka daga gareta.
Sa'i: wani abin awo ne sananne, abin nufi da shi sa'in Annabi, awonsa ya kai nauyi (480) na alkama mai kyau, a lita kuma (lita 3).
Mudun Nabiy: Awo ne na shari'a, shi kuma cikin tafuka biyu ne na mutum madaidaici idan ya cikasu ya miƙe hannunsa da su. Mudun Nabiy shi ne ɗaya bisa huɗu na sa'i da haɗuwar masana fiƙihu, gwargwadansa ML (750).
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

