Asali ga bukukuwan idi, -duk da suna da sunaye dayawa- asali gare su shine kasancewarsu alamomi ga addinai.
الأصل في الأعياد على اختلاف مسمياتها أنها من شعائر الاديان. Asali ga bukukuwan idi, -duk da suna da sunaye dayawa- asali gare su shine kasancewarsu alamomi ga addinai. فهي سمة من السمات التي تتميز بها كل ملة وأتباعها عن غيرهم. saboda haka, bukukuwa alamomi ne da suke banbance kowane addini, da mabiyansa, daga wadanda ba su ba. وقد تواترت النصوص الشرعية بحصر أعياد المسلمين...
Asali ga bukukuwan idi, -duk da suna da sunaye dayawa- asali gare su shine kasancewarsu alamomi ga addinai.
الأصل في الأعياد على اختلاف مسمياتها أنها من شعائر الاديان.
Asali ga bukukuwan idi, -duk da suna da sunaye dayawa- asali gare su shine kasancewarsu alamomi ga addinai.
فهي سمة من السمات التي تتميز بها كل ملة وأتباعها عن غيرهم.
saboda haka, bukukuwa alamomi ne da suke banbance kowane addini, da mabiyansa, daga wadanda ba su ba.
وقد تواترت النصوص الشرعية بحصر أعياد المسلمين في عيدين كل عام. هما الفطر والأضحى
Kuma dalilai na shari'a masu tarin yawa (mutawatirai) sun zo da al'amarin takaice bukukuwan musulmai a kowace shekara cikin biki guda biyu, sune: idin azumi da na lahiya.
وعيد كل أسبوع هو يوم الجمعة.
Shi kuma bikin kowane sati shine idin yinin Juma'a.
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إن لكل قوم عيدا، وهذا عيدنا.
Manzon Allah SAW ya ce: "LALLAI KOWANNE MUTANE SUNA DA BUKI, MU KUMA WANNAN SHINE IDINMU"
وما سوى ذلك من أعياد كالكريسماس ورأس السنة الميلادية وغيرها، فهي لأهل الكتاب.
Duk kuma wani bikin wanda, ba wannan ba, kamar bikin kirsimeti, da wanda ake yi a duk karshen shekarar miladiyya, to wadannan na Yahudawa da Nasara.
ولا يجوز للمسلم اعتبارها ولا الاحتفال بها.
Baya halatta ga Musulmi ya dauke su a ransa a matsayin idi, ko ya yi wannan bikin.
ولا التهنئة بها او المشاركة فيها.
Haka baya halatta, ya taya su murna, ko ya yi tarayya da su a cikinsu.
ويدخل في ذلك: إهداؤهم ما هو من لوازمها،
Yana shiga cikin hakan, (da yake haram), baiwa kafirai kyautar abinda dole ne sai da shi su yi idinsu,
أو بيعهم هذه المستلزمات من أنوار وأشجار. ومأكولات معينة.
ko ya sayar musu wadannan ababen, kamar haske da furanni, da wasu ayyanannun ababen ci (kamar alewa).
فإن هذا منهي عنه لسببين:
Saboda hakan abu ne da aka yi hani akansa, da dalilai biyu:
الأول: إن في ذلك تشبها بهم، وإقرارا لهم على كفرهم، وقد حرم الإسلام التشبه بالكافرين فيما هو من خصائصهم.
Na farko: Lallai cikin hakan akwai, kamantacceniya da kafirai, da kokarin tabbatar da su akan kafircinsu, kuma musulunci ya haramta kamantacceniya da su a cikin abinda ya kebanta da su.
الثاني: إن في هذه الأعياد ابتداعا وإحداثا في دين الله تعالى.
Na biyu: Lallai bukukuwan bidi'a ne, da aka kirkira aka cusa su a cikin addinin Allah Ta'alah.
قال ابن القيم رحمه الله: وأما التهنئة بشعائر الكفر المختصة به فحرام بالاتفاق.
Ibnul Kayyim -Allah ya masa rahama-, yana cewa: Amma gaisuwar taya murna, da alamomin kafirci, wadanda suka kebanta da kafirai, to haramun ne, da ittifakin Malamai.
كأن يهنئهم بأعيادهم. فيقول: عيد مبارك عليك. أو تهنأ بهذا العيد أو نحوه.
Kamar ya taya su murna da zuwan bukukuwan idinsu, ya ce: idinka ya zama mai albarka a gare ka, ko ya ce: ka yi walwalarka da wannan idin (happy new year, happy Christmas), ko magana makamanciyar haka.
فهذا إن سَلم قائله من الكفر، فهو من المحرمات.
Wannan idan mai fadinsa ya kubuta daga kafirci, to lallai fadin hakan yana cikin abubuwa na haramun.
ولا يعني هذا إساءة المعاملة، ولا الاعتداء.
Wannan kuma baya nufin, a munana mu'amala da su, ko a yi musu ta'addanci
فإن رفض المشاركة ليس اعتداء، وإنما هو تميز المسلم واستقلاله في معتقداته وشعائره عن غيره.
saboda kin yin tarayya da su ba ta'addanci ba ne, kawai alama ce da take nuna cewar musulmi ya kebanta daga wanda ba shi ba, a cikin addininsa da akidunsa da alamominsu
ولهذا جاز قبول الهدية منهم.
Shi ya sa, ya halatta, Musulmi ya karbi kyautarsu,
ولا يعد ذلك مشاركة ولا إقرارا للاحتفال.
Kuma ba a kirga hakan, a matsayin tarayya da su cikin bikinsu, ko tabbatar da halaccin bikin.
بل تؤخذ على سبيل البر وقصد التأليف والدعوة إلى الإسلام.
Kawai, za a karbi kyautar ne a matsayin kyautata mu'amala da su, da nufin jansu a jika, da kiransu zuwa ga Musulunci.
ما لم يكن مما ذبحوه لأجل العيد.
Matukar ba kyautar naman da suka yanka, domin bukukuwan idinsu ba ne.
قال شيخ الاسلام ابن تيمية رحمه الله: وأما قبول الهدية منهم يوم عيدهم، فقد قدمنا عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه أنه أُتي بهدية النيروز فقبلها.
Shekhul Islam Ibnu-Taimiyyah Allah ya masa rahama ya ce: Amma karbar kyautarsu a ranar idinsu, to hakika mun gabatar da ambaton cewa lallai an zo da kyautar bikin Nairuz ga Aliyu dan Abiy-Dalib Allah ya kara yarda a gare shi, sai ya karbi kyautar.
File | Action |
---|---|
Asali ga bukukuwan idi, -duk da suna da sunaye dayawa- asali gare su shine kasancewarsu alamomi ga addinai. | Download |
Asali ga bukukuwan idi, -duk da suna da sunaye dayawa- asali gare su shine kasancewarsu alamomi ga addinai.
Scan QR Code | Use a QR Code Scanner to fast download directly to your mobile device