”
#5511HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya…
”
#5512HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi".
”
#5513HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi girman kai a cikin Zuciyarsa, kuma yake takama a Tafiyarsa, zai gamu da Allah yana fushi da shi"
”
#5514HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce: "Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".
”
#5516HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.
”
#5517HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Ayyub Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma . zai ka…
”
#5518HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba…
”
#5519HadeethEnc[Hasan ne]
An Rawaito daga Mu'awiya Bn Haidah -Allah ya yarda da shi ya ce Mazon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Boni ya tabbata ga wanda yake zantar da Mutane sai yayi Karya don Mutane suyi Dariya, Boni ya tabbata a gare shi sannan Boni ya tabbata a ga…
”
#5520HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsir…
”
#5522HadeethEnc[Ingantacce ne ta wani bangaren]
An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"
”
#5541HadeethEnc[Ingantacce ne]
An rawaito daga Anas -Allah yayarda da shi- cewa shi ya ce da Sabit -Allah ya yi masa rahama: bana yo maka Rukya ba da rukyar Manzon Allah -Amincin Allah a gareshi-? ya ce E , yace: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu ma…
”
#5542HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa,…