Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi".
Explanation
Kuma afuwa tare da iko a kan ramuwa ko kama (mai laifin), ba sa karawa mai yinsu komai sai ƙarfi da buwaya.
Kuma wani ba zai ƙanƙan da kai, ya ƙasƙanta ga Allah ba, ba don tsoron wani ba, ba don yaudara (na nuna tausayi) gareshi ba, ba don neman wani abin amfani daga wajensa ba, sai sakamkonsa ya zama ɗaukaka ne da sharafi.
Benefits
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

