Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Wata mata ta zo a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata, bata samu komai awurina ba banda wani dabino ɗaya, sai na bata shi sai ta raba shi tsakanin 'ya'yan nata mata biyu, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo sai ta zantar da shi, sai ya ce: «Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta».
Explanation
Benefits
An so yin sadaka da abinda mutum yake da iko a kansa koda ya zama kaɗan ne.
Tsananin tausayin iyaye ga 'ya'yayensu.
Bayanin halin ɗakunan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa arziƙinsa ya zama tsakatsakiya ne (ya ishe shi).
Bayanin falalar fifita wani akan kai kuma cewa hakan yana daga cikin alamomin muminani; haƙiƙa Nana A'isha - Allah Yarda da ita - ta fifita waccan matar da 'ya'yanta biyu akan kanta, wannan yana nuni akan kyautarta da kuma karamcinta tare da tsananin buƙatuwarta.
An ambaci kyautar 'ya'ya mata da jarraba; saboda abinda ke cikin renonsu na wahala da gajiya, ko saboda wasu mutane suna ƙin su, ko domin cewa yana rinjaya cewa basu da wata hanya ta samun kuɗi da kuma rayuwa.
Musulunci ya zo yana mai tunɓuke al'adun Jahiliyya munana, daga cikin hakan shi ya yi wasicci da 'ya'ya mata.
(Mutum) zai iya samun wannan ladan ko da ta kasance 'ya ɗaya ce kamar yadda ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

