Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara».
Explanation
Benefits
Gaida mara lafiya yana daga haƙƙoƙi tsakanin musulmai, hakan cancanta ga iyalai.
Kwaɗaitarwa ga wanda ya ziyarci mara lafiya ya yi masa wannan addu'ar mai albarka waccea aka ruwaito.
Daga shiryrwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yin magani da ruƙya ta shari'a da Alƙur'ani da kuma addu'o'i masu tsarki, saboda haka tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana yi wa kansa ruƙya idan ya yi rashin lafiya, haka nan yana yi wa wanda ya yi rashin lafiya daga iyalansa da wasunsu ruƙiyya.
Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa yi wa mara lafiya addu'ar waraka tare da abinda ke cikin rashin lafiya na kankare zunubai da lada kamar yadda hadisai suka zo da hakan ya rikitar, to amsa ita ce: Lallai addu'a ibada ce, kuma bata kore lada da kuma kaffara; domin cewa su suna samuwane a farkon rashin lafiyar da kuma haƙuri a kanta, mai addu'a yana tsakanin kyawawa biyu: Kodai abin nufinsa ya samu, ko kuma a canja masa da jawo wani anfanin ko tunkuɗe cuta, kowanne daga cikinsu daga falalar Allah ne.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

