Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu".
Explanation
Benefits
Falalar wuraran zama da a cikinsu akwai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, da ambatan ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa majalisan da a cikinsu babu hakan to sune majalisan zargi ga ma'abotansu a ranar alƙiyama.
Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa ba ne akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin ba tare da ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
Hasara mai faruwa ce garesu a ranar Alkiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin a saɓon Allah.
Wannan gargaɗin idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba da annamimanci da wasunsu?!
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

