Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce: "Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai".
Explanation
Tsarki ya tabbata ga Allah; Tana nufin tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - daga kowace tawaya.
Godiya ta tabbata ga Allah: Siffanta Allah ne da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamashi.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah: Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Allah ne mafi girma: Wato; Mafi girma kuma Mafi buwaya daga dukkan komai.
Kuma cewa falalarta da samun ladanta ba ya nufin sai lallai an jeranta su a yayin furuci da su.
Benefits
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

