Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa
Daga Ammar dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni wata bukata, sai na samu janaba ban samu ruwa ba, sai na tumurmusa a bigire kamar yadda dabba take tumurmusa , sannan na zo wa Annabi - tsira da…

