Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ammar dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni wata bukata, sai na samu janaba ban samu ruwa ba, sai na tumurmusa a bigire kamar yadda dabba take tumurmusa , sannan na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na ambata masa hakan sai ya ce: "Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.
Explanation
Benefits
Halaccin taimama ga wanda ke da janaba bai samu ruwa ba.
Taimama dan babban kari, kamar taimama ne dan karamin kari.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

