Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi
Daga (Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: yaku mutane, lallai ku kuna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lazimci kawunanku wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya}, lallai ni na ji manzon Allah - tsira da ami…

