HadeethEnc · 1.25.0
Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa
Available translations
Choose an available translation of this Hadeeth
01
Hadeeth text
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».
02
Explanation
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa huɗuba, daga cikin abinda ya yi musu wasicci da shi cewa kada tsoro da kwarjinin mutane da kuma ƙarfinsu ya hana musulmi faɗin gaskiya ko umarni da ita idan ya ganta ko ya santa.
03
Benefits
Kwaɗaitarwa akan bayyanar da gaskiya da kuma rashin ɓoyeta dan jin tsoron mutane.
Faɗin gaskiya ba ya nufin rashin lazimtar ladabi ta hanyar faɗinta da kuma hikima da kyakkyawan wa'azi a cikinta.
Wajabcin inkarin munkari, da kuma gabatar da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mas'lahohin mutane waɗanda sukaci karo da ita.

Attribution
[Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi]
Categories
Share
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares