”
#58148HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".
”
#65000HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da ts…
”
#65003HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi -: Lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban kara komai…
”
#65004HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsark…
”
#65044HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su:…
”
#65086HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaid…
”
#65087HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi ma…
”
#65088HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".
”
#65089HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Mahmud ɗan Labid - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Usman ɗan Affan ya yi nufin gina masallaci sai mutane suka ƙi hakan, suka so ya bar shi a kan yadda yake, sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gina masal…
”
#65090HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
”
#65091HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Katada AsSulami - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
”
#65092HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".