Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".
Explanation
Sannan ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan gama kiran sallah, domin cewa wanda ya yi salati ɗaya a gare shi to Allah zai yi masa salati goma da shi, ma'anar salatin Allah ga bawanSa: shi ne YabonSa ga bawa a wurin Mala'iku.
Sannan ya yi umarni da a roƙa masa Allah Wasila - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ita ɗin wani matsayi ne a aljanna, shi ne mafi ƙololuwa, ba ta dace ba, kuma wannan matsayin ba zai samu ba sai ga wani bawa ɗaya daga dukkanin bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, ina ƙaunar in zama ni ne shi, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗa ne, don Tawalu’u; domin cewa idan shi wannan matsayin da yake babba ba zai kasance ba sai ga mutum ɗaya, to, ai wannan mutum ɗayan ba zai zama ba sai shi (Annabin) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin shi ne mafificin halitta.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa wanda ya roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila; to, cetonsa zai same shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Benefits
Falalar salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan amsawa mai kiran sallah
Kwaɗaitarwa a kan roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila bayan salati a gareshi .
Bayanin ma'anar Wasila, da ɗaukakar darajarta ta inda ba ta tabbata sai ga wani bawa ɗaya.
Bayanin falalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da aka keɓanceshi da wancan babban matsayin.
Wanda ya roƙi Allah Wasila ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - to, cetonsa zai ya halatta gare Shi.
Bayanin ƙanƙar da kansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da ya nemi addu'a daga al'ummarsa na wannan matsayin, tare da cewa zai kasance gare shi.
Yalwar falalar Allah da rahamarSa, aikin lada ɗaya (za a yi sakamako) da goma tamkarta.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

