Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Sa'id AlKudri ya ce: Mu'awiya ya fito ga wata halƙa a cikin masallaci, sai ya ce: Me ya zaunar da ku? suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah, ya ce kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, kuma babu wani a matsayina daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi ƙarancin hadisi daga gareni: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: "Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
Explanation
Benefits
Halaccin sa a rantse ba tare da tuhuma ba dan faɗakarwa akan muhimmancin alheri.
Falalar majalisan zikiri da ilimi kuma cewa Allah Yana son su kuma Yana yi wa mala'iku alfahari da su.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

