Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa Bilal yayin sallar Asuba: "Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci, domin ni na ji takun takalmanka a gabana…

