Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - ya ce: Ya ce: "Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana haka…

