Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Explanation
Kuma mafi ƙin garuruwa a wajen Allah sune kasuwanninsu; domin cewa galibi guri ne na algus da yaudara da riba da rantse-rantse akan ƙarya, da saɓa alƙawari, da bijirewa ambatan Allah.
Benefits
Kwaɗaitarwa akan lazimtar masallatai, da yawan kaikawo zuwa garesu, dan neman soyayyar Allah - Maɗaukakin sarki - da yardarSa, da kuma ƙaranta kaikawo zuwa ga kasuwanni, sai dan buƙata; dan nisanta daga faɗawa cikin sabubban ƙiyayyar (Allah).
Imam Nawawi ya ce: Masallatai gurare ne na saukar rahama, kasuwanni kuwa kishiyarsu ne.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

