Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu da wasu kalmomi biyar, sai ya ce: «Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci, Yana ƙasa da ma'au…

