Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu da wasu kalmomi biyar, sai ya ce: «Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci, Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi, ana ɗaga aikin dare kafin aikin rana zuwa gare Shi, da aikin rana kafin aikin dare, shamakinSa shi ne haske, da ace zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinsa ya tiƙe daga halittarSa».
Explanation
Benefits
Allah - Maɗaukakain sarki - Yana ɗaga wanda Ya so kuma Yana ƙasƙantar da wanda Ya so, Yana shiryar da wanda Ya so Yana ɓatar da wanda Ya so daga cikin bayinSa.
Ana ɗaga ayyuka zuwa ga Allah a kowacce rana da kowane dare, a cikin haka akwai kwaɗaitar da bayi su yi muraƙabar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a cikin darensu da kuma yininsu.
Hadisin yana nuni akan adalcin Allah - tsarki ya tabbatar maSa - da kyakkyawan shirya al'amuranSa ga al'amuran halittarSa, babu kokwanto cewa wannan yana daga cikin siffofin cikarSa - Maɗaukakin sarki -.
Tabbatar da shamaki gareShi - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, shi ne kuma hasken da ya tsare tsakaninSa da tsakanin halittarSa, daban dan shi ba da sun ƙone.
Al’Aajurri ya ce: Lallai ma'abota gaskiya suna siffanta Allah - Mai girma da ɗaukaka - da abinda Ya siffanta kanSa - Mai girma da ɗaukaka - da shi, da kuma abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da shi, kuma da abinda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka siffantaShi da shi, wannan (ita ce) mazhabar malamai daga waɗanda ya bi bai yi ƙirƙire ba, Ya ƙare. Ahlus Sunna suna tabbatarwa Allah abinda Ya tabbatarwa kanSa da shi na sunaye da siffofi ba tare da jirkitawa ko korewa ko kaifantawa ko kamantawa ba, kuma suna korewa Allah abinda Ya korewa kanSa, sunayin shiru daga abinda korewa ko tabbatarwa bai zo da shi ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai yawan ji kuma Mai yawan gani}.
Hasken da shi ne siffarSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ba hasken da Ya shamakantu da shi ba ne, hasken da Ya shamakantu da shi haske ne abin halitta, hasken Allah - Maɗaukakin sarki - haskene daya dace da Shi da kuma zatinSa, babu wani tamkarSa, abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi ba wani abu bane sai shamakin da yake kasancewa tsakanin Allah da bayinSa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

