Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci.
Ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku.
Ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku.
Ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku.
Ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku.
Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni.
Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba.
Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba.
Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi.
Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".
Explanation
Kuma Allah - tsarki ya tabbatar masa Yana kiyaye ayyuakan bayi, Yana tsaresu musu su, sannan Ya cika musu su a ranar alƙiyama, wanda ya samu sakamakon aikinsa alheri, to, ya godewa Allah a bisa dacewa da ya yi ga biyayya gareshi, wanda ya samu sakamakon aikinsa wani abu saɓanin hakan, to, kada ya zargi kowa sai zuciyarsa mai yawan umarni da mummuna wacce ta ja shi zuwa taɓewa.
Benefits
Abin da yake faruwa ga bayi na ilimi ko shiriya, to, da shiriyar Allah ne da kuma koyarwarsa.
Abin da yake samun bawa na alheri, to, daga falalar Allah ne - Maɗaukakin sarki -, abin da kuma ya sameshi na sharri, to, daga kansa ne da kuma son ransa.
Wanda ya kayautata, to, da dacewar Allah ne, kuma sakamakonsa falala ce daga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya munana, to, kada ya zargi kowa sai kansa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

