Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayi mana wata huɗuba ba sai ya ce: «Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari».

