Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Ɗan Adam ya cutar da Ni yana zagin zamani alhali Nine zamani, al'amari yana hannunNa iNa jujjuya dare da rana
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Ɗan Adam ya cutar da Ni yana zagin zamani alhali Nine zamani, al'amari yana hannunNa iNa jujjuya dare da rana».
Explanation
Benefits
Ladabi tare da Allah - tsarki ya tabbatar maSa - a magana da kuma ƙudiri.
Wajabcin yin imani da hukunci da kuma ƙaddara, da haƙuri akan cuta.
Cutuwa ba cutarwa ba ne; mutum yana cutuwa da jin mummunan abu ko ganinsa; sai dai cewa hakan ba ya cutar da shi, kuma yana cutuwa da warin da ba'a so kamar albasa da tafarnuwa amma ba sa cutar da shi.
Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Yana cutuwa da wasu daga ayyukan bayinSa munana, sai dai cewa Shi - Maɗaukaki - ba Ya cutuwa da hakan, kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce acikin Hadisi Ƙudsi: «Yaku bayina lallai ku baku isa ku cutar dani ballantana ku cutar daNi, kuma baku isa ku amfanar daNi ba ballatana ku amfanar daNi».
Aibanta zamani da siffanta shi ya kasu gida uku: 1- Ya aibanta zamani akan cewa shi ne mai aikatawa; kuma cewa zamani shi ne mai jujjuya al'amura zuwa alheri ko sharri! to wannan shirka ce babba; domin ƙudircewa ne akan akwai wani mahalicci tare da Allah, kuma domin hakan danganta samar da halittu ne zuwa ga wanin Allah. 2- Ya aibata zamani badan ƙudirce cewa shi ne mai aikatawa ba, kai yana ƙudirce cewa Allah Shi ne Mai yin aiki sai dai yana aibata shi ne domin cewa shi ne mahallin wannan abun abin ƙi a wurinsa; to wannan haramun ne. 3- Ya nufi alheri tsantsa ba tare da zargi ba; to wannan ya halatta, kuma daga gare shi akwai fadin (Annabi) Lud - aminci ya tabbata agare shi -: {Kuma ya ce wannan rana ce mai tsananin wahala}.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

