Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka".
Explanation
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku:
Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri.
Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka.
Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.
Benefits
Bayanin sabubban tsira a duniya da lahira.
Kwaɗaitarwa akan shagaltar mutum da kansa idan ya gajiya daga anfanar waninsa, ko ya ji tsoron cutarwa akan Addininsa da kansa idan ya cakuɗa da mutane.
Nuni zuwa himmatuwa da gida musamman ma dai a lokacin fitintinu, shi yana daga hanyoyi dan kiyaye Addini.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

