”
#3078HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma" Abu Ayyub ya…
”
#3079HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a…
”
#3081HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- yace: wasu yardaddun mutane sun bada sheda a waje na -a guri na wanda yafi kowa a cikinsu shi ne Umar- cewa Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya hana yin sallar nafila marar dalili bayan Asuba har sai rana ta…
”
#3083HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi Bn Amr Bn Al-as -Allah ya yarda da su- "Baya tare da mu wabda duk baya jin tausayin Qaramin mu, kuma bai san girman Babbanmu ba"
”
#3085HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Nu'aman Dan Bashir zuwa ga Annabi: "Wallahi ko dai ku daidaita Sahunku ko kuma Allah ya saba tsakanin Fuskokinku" a wata Riwayar kuma: "Manzon Allah ya kasance yana daidaita sawunmu, har kace yana jera tukwane ne, har sai idan cewa yaga lallai mun fahimce shi, sann…
”
#3086HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".
”
#3087HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin…
”
#3088HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).
”
#3089HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi Dan Buhaina-Allah ya yarda da shi- ya kasance cikin sahabban Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- "Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-yayi musu sallar Azahar sai ya mike daga raka'a biyun farko, bai yi zaman tahiya ba, s…
”
#3090HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: "Na iso akan Jaka, kuma ni a lokacin na kusa Balaga, kuma Manzon Allah SAW yana Sallah da Mutane a Minna ba yana kallon Garu ba, na wuce ta gaban Sahu, sai na sauka, sai na saki Jakar tana kiwo, na shiga Sahu, babu w…
”
#3095HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagas…
”
#3096HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsar…