"Kuna da rakuma dari bakwai tare da su ranar tashin kiyama, dukkansu an yi musu dinki
An rawaito daga Abu Mas'ud -Allah ya yarda da shi- ya ce: wani Mutum ya zo wajen Manzon Allah SAW da Taguwarsa Mai yankakken Kunne, sai ya ce: wannan na bada ita sabida Allah, sai Manzon Allah SAW ya ce: "Kana da Taguwa Dari Bakwai a ranar Al-kiyama dukkansu da linzami"

