Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin".
Wato kwanaki goman, (Zul Hijja) Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah ? Ya ce: Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba.
Explanation
Sahabbai Allah ya yarda da su, suka tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da Jihadi a kwanakin da ba waɗannan goman ba, shin shi ne ya fi ko kuwa ayyuka na ƙwarai a waɗannan kwanakin? saboda abin da suka sani na Jihadi yana cikin mafificin ayyuka.
Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya amsa da cewa kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin sun fi Jihadi a wasu kwanakin, sai dai mutumin da ya fita yana mai Jihadi da kutsawa hatsari da ransa da dukiyarsa; Don ɗaukaka addinin Allah sai ya rasa dukiyar ta sa kuma ran shi ya fita domin ɗaukaka addinin Allah. To wannan shi ne ya fi a kan aiki na ƙwarai a cikin waɗannan kwanaki masu falala.
Benefits
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

