Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani
Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da su - ya ce: Wani balaraben kauye ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ka sanar maganar da zan fada, ya ce: "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin taray…

