”
#5488HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".
”
#5489HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".
”
#5491HadeethEnc[Ingantacce ne]
An karbo daga Abdullahi Bn Mas'ud-Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Ya Allah kamar yadda na kyautata halaye na, haka kuma na kyautata halaye nai"
”
#5502HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".
”
#5878HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Zaid Dan Arƙam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ba zan faɗa muku (komai ba) sai kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana faɗa: Ya kasance yana cewa: «Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro d…
”
#5883HadeethEnc[Hasan ne]
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inci"
”
#5884HadeethEnc[Hasan ne]
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - cewa wani wanda aka ɗorawa fansa ya zo masa, sai ya ce: Haƙiƙa ni na kasa biyan fansa ta to ka taimakeni, ya ce: Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda mazon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da n…
”
#5914HadeethEnc[Ingantacce ne]
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya Manzon Allah yana cewa: "Ya Ubangiji ni ina neman tsarinka daga gajiyawa, da Kasala, da Tsoro, da Tsufa, da Rowa, kuma ina neman tsarinka daga Azabar Kabari, Kuma ina neman tsarinka daga fitinar Rayuwa da ta Mutuw…
”
#5915HadeethEnc[Ingantacce ne]
Daga Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da ni: "ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya
”
#6040HadeethEnc[Ingantacce ne]
Da Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya" kuma cikin wata Riwayar Sufyan Al-Sauri ya ce: Ina kokwanton ni na kara daya daga cikin su.
”
#6047HadeethEnc[Ingantacce ne]
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya ce"Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya"
”
#6072HadeethEnc[Ingantacce ne]
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- cewa Annabi yana yin Addu'a da wadan nan kalmomi:"Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga fitinar Wuta, da Azabar Wuta, da kuma Sharrin Wadata da talauci"