Lallai cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu (suna) tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangiji) al-Rahman, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuyata yadda Ya so
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu (suna) tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangiji) al-Rahman, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuyata yadda Ya so" sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ya Allah Ya mai jujjuya zukata Ka juya zukatanmu a kan biyayyarKa".
Explanation
Benefits
Yana kamata ga musulmi ya dawwamar da roƙon UbangijinSa akan tabbata akan gaskiya da kuma shiriya.
Jin tsoron Allah da rataya da Shi, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya.
Al’Aajurri ya ce: Lallai ma'abota gaskiya suna siffanta Allah - Mai girma da ɗaukaka - da abinda Ya siffanta kanSa - Mai girma da ɗaukaka - da shi, da kuma abinda ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta Shi da shi, kuma da abinda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka siffantaShi da shi, wannan (ita ce ) mazhabar malamai daga waɗanda ya bi bai yi ƙirƙire ba. Nan ya ƙare. Ahlus Sunna suna tabbatarwa Allah abinda Ya tabbatarwa kanSa da shi na sunaye da siffofi ba tare da jirkitawa ko korewa ko kaifantawa ko kamantawa ba, kuma suna korewa Allah abinda Ya korewa kanSa, suna yin shiru daga abinda korewa ko tabbatarwa bai zo akan shi ba, Allah - madaukakin sarki - ya ce: {Babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai yawan ji kuma Mai yawan gani}.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

