Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Akwai darajoji ɗari a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja kamar tsakanin sama da ƙasa ne, Firdausi it ce mafi ƙololuwarsu (a daraja), kuma daga nanne ƙoramun aljanna suke ɓuɓɓugowa, kuma a samanta ne Al’arshi yake. Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi».
Explanation
Benefits
Kwaɗaitarwa akan roƙon Allah Firdausi maɗaukakiya daga gidajan aljanna.
Firdausi ita ce mafi ɗaukakar gidajan aljanna, kuma mafificinsu.
Yana kamata ga musulmi himmarsa ta zama maɗaukakiya, kuma ya yi ƙoƙari ya nemi mafi ɗaukakar matsayai kuma mafifitansu a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Ƙoramun aljanna huɗu su ne ƙoramun ruwa da nono da giya da zuma waɗanda aka ambata a ciki AlƘur'ani a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -; {Kwatankwacin aljannar da aka yi wa masu tsoron Allah alƙawari a cikinta akwai ƙoramu na ruwa ba mai sakewa ba, da ƙoramu na nonon da ɗanɗanonsa bai canja ba, da ƙoramu na giya masu ɗaɗi ga masu sha da ƙoramai na tatacciyar zuma} [Muhammad: 15].
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

