Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».
Explanation
Benefits
Anafni da tashbihi (karantawa) don kusanto da ma'anoni da kuma sharhinsu.
AlƘurɗubi ya ce: Za'a iya cewa to wace buƙata suke da ita na taje kai alhali su matasa ne kuma gashinsu ba ya datti? Kuma wace buƙata ce da su ga tiraren wuta alhali ƙanshinsu ya fi almiski? Ya ce: Za'a amsa da cewa ni'imar 'yan aljanna na ci da sha da tufafi da tirare badan jin raɗaɗin yunwa ba ne ko ƙishirwa ko tsiraici ko wari, kawai su daɗi ne a jere da ni'imomi a jere, kuma hikima a cikin hakan cewa su suna ni'imtuwa da nau'in abinda suka kasance suna ni'imtuwa da shi ne a duniya.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

