Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu,…

