Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".
Explanation
Sai ta kawo hanzarin cewa suna da raƙuma biyu ne, sai mijinta da ɗanta suka yi Hajji akan ɗayan su, kuma ya bar ɗayan dan su yi ban ruwa da shi daga rijiya.
Sai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bata labarin cewa yin Umura a watan Ramadan ladansa ya yi daidai da ladan Hajji.
Benefits
Umra a Ramadan tana daidai da Hajji a lada, ba a sarayar da Hajjin farilla ba.
Ladan ayyuka yana ƙaruwa da ƙaruwar ɗaukakan lokuta, daga hakan akwai ayyuka a cikin Ramadan.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

