Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".

