Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu
Daga Malik ɗan Aus ɗan Hadasan cewa shi ya ce: Na taho ina cewa waye zai canji dirhamomi? sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi alhali shi yana wurin Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da su - ya ce: Ka nuna mana zinarenka, sannan kazo mana, idan ɗan aikinmu ya zo, zamu baka azirfar…

