Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ubadah ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne".
Explanation
Benefits
Hani daga cinikin riba.
Takardun kuɗi suna da hukuncin zinare da azirfa a cikin illar riba.
Siye da siyarwar nau’ukan da riba take shiga cikinsu guda shida suna da halaye: 1- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa daga jinsinsa, kamar zinare da zinare dabino da dabino... to dan (cinikin) ya zama ingantacce an sharɗanta sharuɗɗa biyu: Samun daidaituwa a cikin awon sikeli ko awon kwano, da kuma karɓa a gurin da aka yi cinikin. 2- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa wanda ba jinsinsa ba tare da cewa illar ta zama iri ɗaya, kamar zinare da azirfa, da alkama da sha'ir to a hakan an sharɗanta karɓa, banda samun daidaituwa. 3- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa wanda bana jinsinsa ba tare da samun banbancin illar, to a hakan ba'a sharɗanta karɓa ko daidaituwa ba kamar saida zinare da dabino.
Siyrawa da siyan nau’uka waɗanda riba bata shiga cikinsu, ko ɗayansu riba na shiga cikinsa ɗayan kuma riba bata shiga cikinsa; to ba'a sharɗanta komai ba, ba hannu da hannu ba ba kuma daidaito a awo ba, kamar saida fili da zinare.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

